Labarai
Gwamnatin jihar Yobe ta bayar da umarnin rufe duka makarantun sakandiren kwana saboda barazanar tsaro

Gwamnatin jihar Yobe ya bayar da umarnin rufe duka makarantun sakandiren kwana da ke faɗin jihar saboda barazanar tsaro.
Cikin wata sanarwa da babban darakta yaɗa labaran gwamnan jihar, Mamman Mohammed ya fitar ya ce gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin kare ɗaliban da ke makarantun kwana.
Matakin na zuwa ne bayan da a makon da ya gabata wasu ƴanbindiga suka sace ɗalibai a makarantun kwana jihohohin Naje da Kebbi.
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan taron ƙoli na tsaron jihar da Gwamnan Mai Mala Buni ya jagoranta, domin nazarin tsaron makarantu a wasu sassan ƙasar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa matakin rufe makarantun ya fara aiki ne nan take, har zuwa lokacin da yanayi zai inganta.
Hare-hare kan ɗalibai a makarantu a Najeriya cikin makon da ya gabata, ya haifar da rufe makarantun a wasu jihohin ƙasar da suka haɗa da Neja da Filato da Katsina.
You must be logged in to post a comment Login