Labarai
Gwamnatin Kaduna ta kafa kwamitocin magance ambaliya da Agajin gaggawa

Gwamnatin jihar Kaduna ta ƙaddamar da kwamitoci biyu domin dakile ambaliya da kuma kai agajin gaggawa a daminar bana, a wani bangare na shirin gaggawa da kare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar KADSEMA, Usman Mazadu, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudanar ranar Litinin a jihar ta Kaduna.
Mazadu, ya ce, an kafa kwamitocin ne domin su jagoranci ayyukan ceto da ba da agajin gaggawa, samar da mafaka ga wadanda ambaliya za ta shafa, da kuma tara muhimman kayan agaji cikin lokaci.
Ya ce kwamitocin za su kuma tsara dabarun dakile ambaliya, karfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi, isar da bayanai cikin lokaci ga jama’a da kuma sa ido kan yadda ake gudanar da ayyukan agaji a fadin jihar.
Mazadu ya ce kwamitocin sun ƙunshi wakilai daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, Hukumar Kula da albarkatun ruwa ta Ƙasa NHSA, hukumomin tsaro.
Haka kuma, ya jaddada cewa Gwamna Uba Sani ya himmatu wajen ganin ba a rasa rai ko dukiya sakamakon ambaliya ba, inda ya bayyana kafa kwamitocin a matsayin wani mataki na rigakafi da shiri tun da wuri domin kare al’umma.
You must be logged in to post a comment Login