Labarai
Gwamnatin Kaduna ta kwace wasu gidaje da filaye

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayar da umarnin kwace wasu gidaje da filaye wadanda gwamnatin baya ta raba a cikin harabar makarantu a jihar.
Bayanin kwace filayen na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar, AbdulKadir Muazu Meyere ya fitar.
Sanar ta ce, matakin kwace filayen ya samu amincewa ne tun a bara, kuma tuni an sanar da wadanda aka sayar wa filayen.
Sabon matakin ya shafi makarantu irin su Alhuda-Huda College da ke Zariya da kuma Queen Amina College da ke Kaduna.
Ita ma makarantar Government Commercial College da ke Zariya na daga cikin wuraren da gwamnatin ta kwace filayen su bayan gwamnatin Nasir El-Rufa’i ta sayar da su a baya.
You must be logged in to post a comment Login