Labarai
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin yaƙi da yin Bahaya barkatai

Gwamnatin jihar Kano, ta ƙaddamar da shirin yaƙi da bahaya barkatai a wasu ƙananan hukumomi.
gwamnatin ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da Shugaban Hukumar Samar da Ruwan da Tsaftar Muhalli a yankunan Karkara ta Jihar Kano RUWASSA, Samwilu Abdulkadir Isah, ya fitar.
Ta cikin sanarwar, ya ce, shirin ya shafi ƙananan hukumomin Fagge, Dala, Gwale, Nassarawa, Tarauni, Birni da Kewaye, Garun Malam da Makoda.
Shugaban ya ce, Gwamnan Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya amince da shirin, yayin da ma’aikatan RUWASSA za su riƙa zagayawa domin duba wurare da ɗaukar matakan hana bahaya barkatai.
Gwamnatin ta kuma fara shirye-shiryen gina bandakuna a makarantun tsangaya, yayin da RUWASSA za ta duba wuraren da ke fama da gurɓataccen ruwa tare da kai ɗauki da karɓar bayanai daga jama’a.
You must be logged in to post a comment Login