Connect with us

Labaran Kano

Gwamnatin Kano ta kwace gurbatattun magunguna a kasuwar Dan-Gwauro

Published

on

Kwamitin gwamnatin Kano mai aikin tsaftace tashoshin mota da kasuwanni, wuraren taruwar jama’a da kuma yaƙi da kayan maye, ya ƙwato tarin miyagun ƙwayoyi da gurɓattu har ma da na Jabu a kasuwar sayar da magunguna da ke Ɗan-Gwauro a nan Kano.

 

Kwamitin ya yi wannan aiki ne a daren Talatar makon nan yayin da ya kai ziyara kasuwar bayan da shugaban kasuwar ya sanar da gwamnatin Kano cewar za su mika mata ƙwayoyin domin ta lalata su.

 

Kwamitin ya balle wani dakin ajiyar kayayyaki da ke ofishin shugaban kasuwar ne, inda ya same shi makare da wasu miyagun kwayoyi na fiye da Naira biliyan 1.

 

A yayin ziyarar, shugaban kasuwar Alhaji Husaini Labaran Zakari, ƴa ki amincewa ya bude dakin da suka adana miyagun kwayoyi,  bayan da ya bayar da wasu masu tarin yawa da suka hadar da wadanda wa’adin amfaninsu ya ƙare da na Jabu, waɗanda kuɗin su ya haura naira biliyan ɗaya da miliyan dari biyar.

 

Da ya ke jawabi bayan karbar magungunan, shugaban kwamitin Manjo Adamu Abubakar Usman mai ritaya, ya bayyana cewa, sun karbi kayan wadanda aka cika babbar motar dakon kaya watau Trailer, Inda za su miƙa su ga gwamnatin jihar Kano, domin ta ɗauki matakin da ya dace a kansu.

 

A ganawar sa da manema labarai, shugaban kasuwar Alhaji Husaini Labaran Zakari, ya ce, wasu daga cikin magungunan da suka bai wa gwamnatin sun ƙwato su ne yayin da wasu kuma daga ciki masu su ne suka kai musu su domin raɗin kansu bayan da wa’adin aikin su ya kare.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!