Labarai
Gwamnatin Kano ta aike da sunayen mutum 2 zuwa majalisa domin tantance su a matsayin sabbin kwamishinoni

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tura sunayen Barrister Abdulkarim Kabir Maude, da Dr. Aliyu Isa Aliyu zuwa majalisar dokokin jiha domin tantancewa a matsayin kwamishinoni da kuma mambobin majalisar zartarwa ta jiha.
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Asabar.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa na da niyyar ci gaba da zabar matasa masu kwarewa da kishin ci gaban jiha, tare da mayar da hankali kan nagarta, cancanta da gaskiya a shugabanci.
You must be logged in to post a comment Login