Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano ta bada wa’adin mako 2 ga masu aikin sabin ta asibitin Nuhu Bamalli

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bada wa’adin mako biyu ga ɗan kwangilar da yake aikin gyara asibitin Nuhu Bamalli da ke ƙaramar hukumar Birni, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma ke kokawa kan yadda asibitin ya shafe watanni uku ba tare da an kammala aikin ba.

Kwamishinan ayyuka na jihar Injiniya Marwan Ahmad ne ya bayyana hakan yayin ziyarar gani da ido da ya kai asibitin a yau, inda ya ce la’akari da yadda al’umma ke ta kokawa kan yadda masu aikin suka dakatar da yin aikin ya sanya gwamnati ta dau wannan matakin domin a dawo da martabar asibitin kamar yadda aka sanshi a da.

Marwan ya ƙara da cewa labarin da suka samu shine wai ƴan kwangilar sun tafi hutune wanda hakan ya dakatar da aikin, sai dai kuma yanzu haka zasu mayar da hankali wajen ci gaba da aikin cikin wa’adin da aka ba su.

Ya ƙara da cewa za’a fara aiki da inda aka kammala cikin gaggawa domin samarwa da al’ummar jihar kano sauki.

Habibu Dalhatu Zango shine ɗan kwangilar da yake kula da aikin asibitin yayiwa manema labarai ƙarin haske kan yadda aka sami tseko a aikin.

Inda ya ce matsalar daga gare su take a dan haka yanzu zasu mayar da hankali wajen sunyi aikin cikin makwannin da gwamnati ta ba su.

Haka kuma gwamnatin Kano ta ce cikin wa’innan makwannin da aka bawa ɗan kwangilar in ya gaza ƙarasa aikin zata sallame shi ta bawa wanda zasu kammala cikin gaggawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!