Labarai
Gwamnatin Kano ta bayar da tallafin kayan abinci ga jami’an tsaro
Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da rabon kayan abinci ga jami’an tsaro da suke aiki a jihar.
Gwamnatin ta kuma ce, za ta ci gaba da bayar da tallafin ga sauran al’ummar gari harma da masu buƙata ta musamman domin suma su amfana da rabon kayan abincin da gwamnati take yi na rage raɗadin janye tallafin mai ta akayi
Sakataren gwamnatin jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi ne ya jagoranci bayar da tallafin ga hukumomin tsaron da masu buƙata ta musamman da yammacin Litinin a wajen da aka ware domin ajiyar kayan abincin gwamnati dake kan titin Maganda
Baffa Bichi ya kuma ce wannan rabon kayan ya biyo umarnin da gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayar domin a bayar ga iyalan ga marayu na jami’an tsaron
Cikin jami’an da aka bawa kayan sun haɗar Police, Custom,Civil Defence, Immigration Land Army, Nevy, Air Force, Vigilante da dai sauran hukumomin tsaro
Sai dai tuni kayan suka isa ga hannun jami’an tsaron inda suka bayyana farin cikin su kan yadda gwamnatin kano ta tuna da su musamman iyalen wasu daga cikin jami’an tsaron da suka rasa mazajen su
Gwamnatin kuma ta ƙaddamar da bayar da tallafin ga masu buƙata ta musamman da suka hadar da masu lalular gani, ji, tafiya, marasa lafiyar ƙwaƙwalwa da zabiya da dai saura masu buƙata ta musamman
Inda suma suka fara karɓar kayan nasu ba da ɗaukan lokaci ba, inda suma suka bayyana jin daɗin su kan yadda gwamnatin tazo musu da nasu tsarin wajen bayar da tallafin gare su
Inda gwamnatin tace suma baza’a manta da su ba kasancewar suma al’umma ne da suke da hakki dan haka gwamnatin taga tacewar yi musu tsari wajen basu wannan tallafin na kayan abinci
Za’a bawa ko wacce ƙaramar hukuma adadin buhu dubu ɗaya cikin ƙananan hukumomi 44 domin rabawa masu buƙata ta musamman
You must be logged in to post a comment Login