Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano ta ce a shirye ta ke na ganin ta kammala dukkanin aikin cigaban kasa
Gwamnatin Jihar Kano ta ce a shirye ta ke wajen ganin ta kammala dukkannin aikin ci gaban kasa kamar yadda ya ke kunshe cikin tsare-tsaren kayyadajjen lokaci na kasafin kudin bana.
Kwamishiniyar Kasafi da tsare-tsare ta Jihar Kano Hajiya Aishatu Ja’afar Yusuf ce ta sanar da hakan lokacin da ta ke kaddamar bude taron bita na kwanaki biyar ta ma’aikatar ta shirya.
Bitar za ta maida hankali kan batun Sufuri da samar da ruwan shad a raya karkara, har ma da bunkasa rayuwar mata da matasa da kuma mutane masu bukata ta musamman, tare da hadin gwiwar hukumomin kula da ayyukan Jiha da na kananan hukumomi da Bankin Duniya da Turai da aka gudanar jiya a Kaduna.
A gefe guda kuma kwamishinan Albarkatun Ruwa Alhaji Usman Sule Riruwai ya ce ma’aikatarsa ta yi nisa wajen samar mafita dangane da matsalolin karancin Ruwan sha a Kano.
Cikin wata sanarwa mai kunshe da sa-hannun jami’in yada labaran ma’a’ikatar Adamu Abdullahi, ta ce kwamishinan ya bukaci mahalarta bitar su maida hankali wajen ganin sun koyi abinda aka shirya koya mu su domin ciyar da Jihar Kano gaba