Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun shirya ci gaba da gyaran hanyoyin karkara – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin ci gaba da gyaran hanyoyi da kuma inganta wutar lantarki a cikin karkara.
Kwamishinan raya karkara da da ci gaban al’umma na jihar Musa Iliyasu Kwankwaso ne ya tabbatar da hakan, jim kadan bayan kammala shirin Baraka da Hansti na nan Freedom Radio.
Musa Ilyasu ya ce dama tuni gwamnatin Kano ta fitar da tsare-tsare na ayyukan ci gaba da za’a yi a wasu daga yankunan Karkara na jihar Kano.
Sai dai ya ce bullar annobar Corona ta janyo dakatar da ayyukan ci gaba da aka tsara faraway a yankunan karkara a nan Kano
Kwamishinan ya Kuma ce rashin isassun kudade na kawo cikas a wajen gudanar da tarin ayyukan da gwamnatin jihar Kano ta tsara gudanarwa.
Musa Iliyasu Kwankwaso yayi Kira ga al’ummar da suke fuskantar matsalar rashin kyan Hanyoyi da sauran kayan more rayuwa da su Kara hakuri, yana mai cewa ma’aikatar a shirye ta ke ta kara inganta rayuwar mutane mazauna karkara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!