An Tashi Lafiya
Gwamnatin Kano ta ce ana cigaba da samun nasara a ƙoƙarin ta na daƙile cutar Amai da Guda
Gwamnatin jihar Kano ta yi ƙarin bayani kan halin da ake ciki game da annobar amai da gudawa, wadda ta ɓullo a wasu yankunan jihar.
A kwanakin baya, aƙalla ƙananan hukumomi 22 ne ke ɗauke da annobar, daga bisani kuma suka koma ƙananan hukumomi 16, sai kuma ƙananan hukumomi 10, sannan a yanzu haka kuma suka koma ƙananan hukumomi 6 kacal ɗauke da annobar.
Kwamishinan lafiya na Jiha Dr Aminu Ibrahin Tsanyawa ne ya bayyanawa Freedom Radio cewa, daga cikin mataken da gwamnati ta ɗauka akwai faɗakarwa akan yadda al’umma za su rinƙa kula da jikin su da kuma abincin su, wanda hakan yasa yayi tasiri matuƙa wajen daƙile cutar.
Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa, ba sa karɓar kudi daga wajen masu fama da cutar ta Amai da gudawa, illa ma dai suna basu magunguna kyauta.
You must be logged in to post a comment Login