Coronavirus
Gwamnatin Kano ta ce sai an bullo da wasu matakai kafin a bude makarantu
Gwamnatin jihar Kano ta ce sai an bullo da wasu matakan da ta gamsu da su kafin a bude makarantu a fadin jihar.
Kwamishinan yada labarai na Kano Muhammad Garba ne ya bayyana hakan, yayin zantawarsa da Freedom Radio.
Kwamishinan ya ce kwamitin koli kan yaki da cutar Covid-19 na kasa ya bukaci ma’aikatar ilimi ta jihar Kano da ta fito da matakan da suka dace wadanda zasu sanya a bude makarantu Boko da na Islamiyya.
Muhammad Garba ya ce sai kwamitin ya gamsu da matakan da gwamnatin Kano ta gabatar kafin a basu izinin bude makarantun, la’akari da yadda ake fama da annobar Covid-19 mai saurin yaduwa.
“Gwamnati ta kanyi la’akari da abubuwan da suke faruwa, saboda haka, kamar yadda na sani ana nan ana bin ka’idoji a jiharmu, don haka ina tabbatarwa da al’ummar Kano cewa gwamnati za ta yi duba na tsanaki a kai”. In ji shi
A rana 12 ga watan Yunin 2020 ne gwamnatin jihar Kano ta fitar da sanarwar cewa ta bude dukkanin gidajen kallo da ke fadin jihar, bayan da aka samu sassaucin cutar Covid-19.
You must be logged in to post a comment Login