Connect with us

Labaran Kano

Gwamnatin Kano ta fara raba kwandinan shara ga masu adaidaita sahu

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta fara raba kwandinan zuba shara ga masu tuka baburan adaidaita sahu a sassan kwaryar birnin Kano, a wani mataki na kara inganta tsafta da kare muhalli. Wannan shiri na daga cikin kokarin gwamnati na dakile yawaitar zubar da shara ba bisa ka’ida ba, musamman a manyan hanyoyi da wuraren da jama’a ke yawan zirga-zirga.

Shugaban Hukumar Kwashe Shara da Tsaftar Muhalli ta Jihar Kano, Dakta Muhammad S. Khalil, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da Freedom Radio da safiyar yau. Ya ce an dauki wannan mataki ne domin bai wa masu tuka adaidaita sahu damar tara shara cikin tsari, maimakon jefar da ita a kan tituna ko magudanan ruwa, wanda ke haddasa gurbacewar muhalli da barazanar lafiyar al’umma.

Dakta Khalil ya kara da cewa gwamnati na fatan wannan shiri zai taimaka matuka wajen tsaftace birnin Kano tare da karfafa wayar da kan jama’a kan muhimmancin kiyaye muhalli. Ya kuma bukaci hadin kan masu tuka adaidaita sahu da sauran al’umma wajen amfani da wadannan kwanduna yadda ya dace, domin cimma burin samar da birni mai tsafta da ingantaccen muhalli ga kowa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!