Coronavirus
Gwamnatin Kano ta gana da Telolin da za su yi aikin dinka “Face Mask”
Kwamitin kar ta kwana kan yaki da cutar Corona a Kano ya bukaci kungiyoyin telolin da za suyi dinkin takunkumin fuska da Gwamnatin Kano ta bayar suyi aikin cikin tsafta saboda yanayin Corona.
Shugaban kwamitin kuma mataimakin Gwamnan Kano Nasir Yusuf Gawuna ne ya bayyana hakan a yau lokacin da Gwamnan Kano ke kaddamar da baiwa kungiyoyin Teloli dinkin takunkumin fuska.
Ya kara da cewa jami’an lafiya zasu kuma samarwa da telolin kayan tsaftace da kansu da hana daukar cuta yayin dinkin.
Wasu daga cikin shugabannin kungiyoyin Telolin sun bayyana za suyi aikin cikin nagarta.
Da yake jawabi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce sun baiwa telolin aikin dinkin ne domin Samar musu aikinyi a wannan yanayi na Corona
Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya ce zasu kuma cigaba da baiwa telolin aikin domin rabawa alummar Kano dan karesu daga Corona.
Karin labarai:
Covid-19: Abinda yasa ake samun “0 Case” a Kano
You must be logged in to post a comment Login