Kasuwanci
Gwamnatin Kano ta hana yan gwangwan sayo karafa daga jihohin Arewa maso Gabas

Gwamnatin jihar kano ta umarci masu gudanar da sana’ar gwangwan a da su dakatar da sayo kayayyakin daga yankin Arewa maso Gabas sakamakon iftila’in da aka samu a kwanan na abubuwan fashewa a cikin kayan gwangwan da suke da alaƙa da yankin.
Kwamishinan tsaro na jihar Kano AVM Ibrahim Umaru mai ritaya ne ya bayyana hakan a yau yayin wata ganawa da ƙungiyar masu sana’ar gwangwan reshen Arewa kan irin iftila’in da ya faru a Kano sakamakon kayan gwangwan din.
AVM Ibrahim Umaru ya ƙara da cewa an ɗauki wannan mataki ne domin kare rayukan da dukiyoyin al’ummar Kano.
Da ya ke jawabi, shugaban ƙungiyar masu sayar da kayan gwangwan na yankin Arewa Alhaji Aminu Hassan ya ce, sun gamsu da umarnin da gwamnatin kano ta bayar na dakatar da shigo da kayan daga yankin Arewa maso Gabas domin kare jihar kano daga barazanar tsaro.
Kwamishinan ya kuma gargadi mambobin ƙungiyar da su kasance masu bin umarnin da aka basu domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login