Kasuwanci
Gwamnatin Kano ta haramta amfani da injinan sare Bishiyu ba bisa ka’ida ba

Gwamnatin Jihar Kano ta haramta yin amfani da injina wajen sare Bishiyu ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.
Kwamishinan ma’aikatar Muhalli da sauyin yanayi Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan a yau Talata yayin wani taron manema labarai da ma’aikatarsa ta kira domin faɗakar da al’umma kan wannan sabon mataki da gwamnati ta ɗauka domin daƙile matsalar yawan sare bishiyu barkatai ba bisa ka’ida ba, lamarin da ke zama barazana ga muhalli.
Kwamishinan, ya ce, daga yau duk wanda aka samu da laifin sare bishiya ba bisa ƙa’ida ba ta hanyar yin amfani da injin zai biya tarar naira dubu dari biyu da Hamsin 250,000 ko kuma Dubu Dari Biyar 500,000 ko har ma da iya tura shi gidan gyaran hali.
Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya kara da cewa, ” A dauki wannan mataki ne domin kare muhalli daga barazana da kuma matsalolin sauyin yanayi bisa la’akari da yadda a wannan lokaci al’umma ke yanke bishiya ba bisa ƙaƙida ba”.
Haka kuma, ya kara da cewa, “Don haka duk wanda ya ke yin anfani da injin yanke bishiya ya zama wajibi ya zo ma’aikatar nan ya nemi sahalewa domin sanin irin ayyukan da zai rika yi da shi kamar yadda tsarin amfani da shi ya tanadar”.
“Sannan, muna kara yin kira ga daukacin al’umma da ma’aikatu da hukumomi har ma da makarantu da su tabbatar da cewa ana bin wadannan dokoki yadda ya dace domin kare muhalli daga matsaloli da kuma barazanar da ya ke fuskanta”, Inji Dahiru Muhammad Hashim.
Kwamishinan na ma’aikatar Muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano, ya kara da cewa, wadannan dokoki na cikin tanade-tanaden hukunta laifuka na kasa da na jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login