Labarai
Gwamnatin Kano ta haramta yunkurin kafa sabuwar hukumar Hisbah

Gwamnatin Jihar Kano ta haramta yunkurin kafa wata sabuwar hukumar Hisbah da ake kira “Hisbah Fisabilillah” a jihar, tana mai gargadin cewa duk wanda aka samu yana amfani da sunan doka zata yi aiki akan sa inda aka bada umarni ga jami’an tsaro da su kama duk wani dake yunkurin anfani da sunan.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Kwamrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan da yammacin juma’ar nan yayin wani taron manema labarai da aka kira, inda ya bayyana cewa gwamnati bata amince da wata sabuwar hukumar Hisbah ba face wadda doka ta kafa a jihar.
Kwamishina Waiya Ya ce gwamnati ta samu rahotanni game da wasu mutane da ke ƙoƙarin kafa sabuwar hukumar ta Hisbah a ƙarƙashin sunan “Fisabilillah”, lamarin da ya saba wa doka kuma yana iya jefa tsaro cikin haɗari.
You must be logged in to post a comment Login