Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano ta ja kunnen mutane kan amfani da wuta a lokacin hunturu
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci jama’ar jihar da su rika kula da yadda su ke mu’amala da wuta a wannan lokaci na hunturu don kaucewa hadarin gobara.
Babban mataimakin na musamman ga gwamnan Kano kan takaita yaduwar masifu Alhaji Idi Bukar ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa.
Sanarwar ta kuma bukaci jama’a da a duk lokacin da aka dauke wutar lantarki su gaggauta kashe na’urorin lantarki da kuma gayyato kwararrun masu gyaran wuta da su rika duba musu ko ya Allah wata matsala ta faru sanadiyar wayar lantarki.
A cewar Idi Bukar ta cikin sanarwar dai, jama’a su daina barin kananan yara na dafa abinci da kuma kashe wuta a duk lokacin da aka gama dafa abinci, yayin da ya kuma ya kuma shawarci shugabannin kasuwanni da su rika kula da tsaron kasuwanninsu cikin dare.