Coronavirus
Da dumi – dumi: Gwamnatin Kano ta janye dokar kulle
Gwamnatin jihar Kano ta janye dokar kulle da aka dauki sama da watanni uku ana yi sakamakon Covid-19.
Biyo bayan rahotannin da aka gabatar a fadar gwamnatin Kano na samun nasara akan yaki da Corona a Kano gwamnatin ta sanar da janye dokar.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan bayan ya karbi rahoton halin da ake ciki a Kano a yanayi na Corona.
Gwamnan ya ce zirga-zirga rika kasancewa ne daga karfe goma na dare zuwa hudu na safiya,.
Ya kuma ce ma’aikatan gwamnati da ke 12 za su fara zuwa aiki daga Litinin din nan, kuma za su rika fita aiki da misalign karfe tara na safe zuwa karfe biyun rana.
Abdullahi Ganduje ya ce masu adai-dai-ta sahu ba a lamunce msu su dauki sama da mutum biyu ba, duk wanda aka samu da karya doka za a gurfanar da shi gaban kotun tafi-da-gidanka.
You must be logged in to post a comment Login