Labarai
Gwamnatin Kano ta kafa kwamatin binciken yadda gwamnatin Ganduje ta siyar da kasuwar siyar da nama ta Abbatuwa dake Chalawa

Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamatin mutane 9 da zai binciki yadda gwamnatin Ganduje ta siyar da kasuwar sayar da Nama ta Abbatoir dake rukunin masana’antu ta Chalawa tare da kayan ta.
Barista Muhyi Magaji Rimin Gado tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasha ta Kano ne dai zai jagoranci kwamatin.
Da yake karin haske Sakataren gwamnatin Kano Umar Faruk Ibrahim ya ce an kashe sama da naira biliyan Ashirin wajen siyan kayan dake cikin kasuwar a baya amma aka sayar dasu kasa da miliyan 10 har da filin gurin.
Da yake jawabi shugaban kwamatin Barriester Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce za su yi aiki tukuru wajen tabbatar da sunyi abin da ya kamata.
An dai baiwa kwamatin wa’adin makonni uku da ya mika rahoton sa GA gwamnatin ta Kano.
You must be logged in to post a comment Login