Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano ta karya rahotannin da ke cewar hukumar EFCC ta bukaci binciken Hafsat Ganduje
Gwamnantin jihar Kano ta ce umarnin da wata babban kotun birnin tarayya Abuja ta bayar na bukatar hukumar EFCC ta gaggauta bincika maid akin gwamnan jihar Kano Hajiya Hafsat Ganduje ba gaskiya bane.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan shari’a na jihar Kano Barista Ibrahim Mukhtar ya sanyawa hannu a jiya litinin ta musanta zance inda ta ce wani yunkuri ne na bita da kulli ga matar gwamnan..
Ya ce wannan wani shiri ne na masu adawa da ci gaban jihar Kano suka shirya da kuma ‘yan siyasar da suke kokarin ganin kawo nakasu a gwamnantin jihar.
Barista Ibrahim Mukhtar ya kara da cewa, an shigar da karar ne tun Nuwambar shekarar 2018 inda kotun ta ware 10 ga watan Disamba a matsayin ranar saurarar, amman ba wanda ya zo ko kuma ya wakilci masu shigar da karar.