Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta musanta rahoton yara Miliyan 2 da ke bara, Ta buƙaci ƙungiya ta janye rahoton

Published

on

Gwamnatin Kano ta hannun Hukumar Ƙididdiga ta jihar  KSBS, ta musanta iƙirarin cewa, sama da yara miliyan 2 ne ke rayuwa a matsayin mabarata a titunan Kano, tana mai bayyana adadin a matsayin maras tushe kuma saɓanin bayanan hukuma.

A wata sanarwa da Darakta Janar na hukumar ta KSBS Dakta Suraj Sulaiman, ya fitar a yau Litinin, hukumar ta ce rahoton da wata ƙungiya mai zaman kanta, Global Improvement of Less Privileged Persons Initiative GIOPPINI, ta wallafa bai yi dai-dai da sakamakon binciken da hukuma ta gudanar ba a ƙananan hukumomi takwas na birnin Kano.

KSBS ta bayyana cewa a bincikenta na taswira da ta gudanar, ta gano jimillar mabarata 6,573 ne kacal, inda yara masu shekaru daga 0 zuwa 10 suka kai kashi 7 cikin ɗari watau su 457, yayin da matasa masu shekaru 11 zuwa 20 suka fi yawa da kashi 56.4 cikin ɗari.

Hukumar ta ce sakamakon binciken ya nuna cewa matsalar ta fi alaƙa da talauci, rashin aikin yi da ƙarancin ilimi, ba wai yawan yara ƙanana kamar yadda aka bayyana a rahoton ƙungiyar ba.

Haka kuma hukumar, ta kuma jaddada cewa, talauci ne babban dalilin bara a jihar.

KSBS ta kuma tunatar da cewa duk wata ƙungiya da ke son gudanar da bincike a Kano dole ne ta nemi amincewar hukuma tun kafin fara aiki, inda ta bukaci ƙungiyar ta GIOPPINI ta fito fili ta nuna sahalewar da aka ba ta, idan har akwai.

Hukumar ta bai wa ƙungiyar wa’adin sa’o’i 48 ta janye rahoton tare da gyara kuskuren da ta wallafa, in ba haka ba za ta bi hanyoyin shari’a.

Sai dai ta amince cewa bara babbar matsala ce, ta na mai cewa dole ne a yi amfani da sahihan bayanai wajen tsara manufofi, musamman duba da matakan da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta ɗauka na farfaɗo da ilimi da rage raunin yara da matasa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!