Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Gwamnatin jihar Kogi ta karyata NCDC kan bullar Corona a jihar

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta musanta rahoton hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC cewa mutum biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ta NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an samu bullar cutar Covid-19 a jihar ta Kogi inda tace mutane 2 ne ta tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dakta Saka Haruna Audu ya musanta rahoton, inda ya fitar ta bayyana rahoton na NCDC a matsayin labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe balantana makama.

Dakta Saka Audu ya ce a shirye gwamnatin Kogi ta ke wajen kare rayukan al’ummarta, kuma ba za ta sanya siyasa a cikin sha’anin kiwon lafiya a jihar ba.

Har zuwa wannan lokaci 3:20pm da muke hada muku wannan labari hukumar NCDC bata ce komai ba game da ikrarin na gwamnatin jihar Kogi.

Labarai masu alaka:

Coronavirus ta bulla a jihar Kogi

Wadanda suka kamu da Corona sun kai 936 a Kano

Idan zaku iya tunawa dai an kwashe tsawon lokaci bayan bullar cutar Corona a Najeriya, ana dambarwa tsakanin gwamnatin jihar Kogi da kuma hukumar ta NCDC wadda har ta kai a baya gwamnatin jihar taki amincewa jami’an hukumar su shiga jihar ta, inda kwamishinan yada labarai na jihar Kingsley Fanwo yace sai an fara yiwa jami’an NCDC din gwajin cutar kafin su gudanar da aikin su a jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!