Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano ta rantsar da kantomimin ƙananan hukumomi 44

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rantsar da kantomimin ƙananan hukumomi 44 dake faɗin jihar Kano inda gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya buƙaci dukkanin shugaban nin da aka rantsar da su tabbatar sunyi wa al’ummar yankunan su ayyukan da ya kamata.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne da yammacin jiya jim kaɗan cebayan rantsar shugabannin riƙon a ɗakin taro na Coronation dake fadar gwamnatin Kano.

Gwamnan ya kuma ce za su sanya idanu akan dukkanin nin shugabannin ruƙon domin ganin sunyi wa al’umma aiki yadda ya kamata.

Ya ƙara da cewa lalacewar ƙananan hukumomi da aka sani a baya yana fatan zasu tabbatar sun farfaɗo da su

Wasu daga cikin kantomimin da aka rantsar su ce zasu tabbatar sunyiwa al’umma aikin da ya kamata domin ƙara daga darajar kananan hukumomi.

Gwamnatin kano tace ya zama wajibi aga canji a ƙananan hukumomi 44 bisa wannan naɗi da akayi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!