Labarai
Gwamnatin Kano ta sabunta kwangilar aikin hanya a kan Naira biliyan 12

Gwamnatin Jihar Kano ta sabun ta kwangilar hanyar da ta tashi daga Kankare zuwa Karaye ta kuma ta hada kananan hukumomin Tofa da Rimin Gado da Kabo da Karaye a kan kudi Naira biliyan goma sha biyu, wadda gwamnatocin baya suka yi watsi da ita.
Kwamishinan shari’a na Kano Barista Haruna Isah Dederi, ne ya sanya hannu a wajen sabunta aikin a madadin gwamnatin.
Barista Haruna Isah Dederi ya ce, idan aka kammala aikin hanyar zai taimaka wa al’ummar da ke makwabtaka da ita musammam ta bangaren ci gaba da habakar tattalin arziki.
A nasa jawabin mataimakin shugaban majalisar dokokin Kano Muhammad Bello Butu-butu cewa ya yi majalisar dokokin Kano, za ta dinga bibiyar aikin don ganin kamfanin da aka bai wa ya yi shi yadda ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login