Labarai
Gwamnatin Kano ta sanya hannu kan dokar yin gwaji kafin Aure
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar da ta wajabta yin gwaje-gwajen lafiya ga duk masu niyyar yin aure a faɗin jihar.
Hakan na nufin cewa daga yanzu babu wani aure da za a ɗaura a jihar har sai an gabatar da takardar sakamakon gwajin ƙwayoyin halittun gado, da na cutar hanta (Hepatitis B da C), da na ƙwayar cuta mai karya garkuwar jiki (HIV).
Gwamnan ya sanya hannu kan dokar ne kimanin mako guda bayan majalisar dokokin jihar ta amince da ita.
A cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa an bijiro da dokar ne domin rage yawan yaran da ake haihuwa ɗauke da wasu cututtuka da ake iya ɗauka ko kuma gadonsu daga iyaye, kamar cutar sikila da HIV da kuma ciwon hanta.
Haka nan dokar ta haramta tsangwamar mutane masu fama da cutar HIV ko sikila ko kuma cutar hanta.
Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 13 ga wannan wata na Mayu, 2024.
You must be logged in to post a comment Login