Labarai
Gwamnatin Kano ta sha alwashin inganta walwalar daurarru dake gidan gyaran hali

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta duba hanyoyin inganta mutanen da iftila’i rayuwa ya kaisu gidan gyaran hali daban-daban a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci gidan ajiya da gyaran hali dake janguza a nan Kano da yammacin yau Jumma’a.
Abba Kabir yasha alwashin tabbatar da tsari mai kyau da za’a koyar da matasan sana’oi kafin karewar wa’adinsu a gidan, tare da tabbatar da ingancin abinci, bandakuna da kuma dakunan baccinsu da ilimin harma da Addini.
Ziyarar ta biyo bayan wani rahoto da wata jarida ta wallafa a baya bayan nan, inda aka zargi rashin isasshen abinci da laifukan lalata tsakanin fursunoni a wadannan gidajen gidan gyaran halin.
You must be logged in to post a comment Login