Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsare masu kananan laifi shike kawo cinkoso a gidan gyaran hali-PRAWA

Published

on

Mataimakin babban kwantorala na gidan gyaran hali na Kano, Garba Mu’azu Chiranchi, ya ja hankalin al’ummar jihar Kano da su rika bin dokokin da gwamnati ta shimfida na takaita zirga zirga don hana cinkosan jama’a a gidan yari.

Garba Mu’azu Chiranchi ya bayyana hakan ne yayin da kungiyar dake sanya idanu kan walwalar mutanan dake daure wato Prisoners Rehabilitation and Welfare Action, (PRWA) ta kai shalkwatar hukumar gyaran halin don kula da yadda mutanan da aka kama da kananan laifukan suke gudanar da ayyukan da aka san yasu.

Ya kuma ce mutanan da aka kama da kanann laifuka za su rika zuwa suna gudanar da ayyuka duk lokacin da aka bude gari kuma zasu kwashe tsawon watanni biyu suna ayyukan.

Anyi wa dan wasan Ac Milan Castillejo Fashi a Italiya

Mataimakin gwamnan Bauchi ya warke daga Corona cikin kwana bakwai.

Da take jawabi shugabar kungiyar dake  saka idanu kan walwar mutanan da aka daure Hajiya Kaltume Oboirien, ta ce a koda yaushe kungiyar na duba yadda ya kamata ace mutanan da suka aikata kananan laifuka ba’a tsare su ba inda tace kamata yai ayi musu tara.

Wasu daga cikin mutanan da aka kama sun bayyana nadamar su, inda suka sha alwashin cewa bazasu kara yiwa dokar gwamnati karan tsaye ba.

Akalla an kama sama da mutane arba’in a ranar Asabar din data gabata sabo da aikata laifuka daban-daban da suka hadar da hada tarukan Biki da na yawo a gari da dai sauran su harma akai musu daurin Talala.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!