Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta yi gargadi kan matakan tsaftar muhalli a Abbatuwa

Published

on

Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi da Albarkatun Ruwa ta Jihar Kano ta bukaci ’yan kasuwar Abbatuwa da su kwashe shara da kuma kashin dabbobin da suka tara, tare da share magudanan ruwan kasuwar.

Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan a yau Juma’a, yayin duban tsaftar muhalli a kasuwanni, ma’aikatun gwamnati, har ma da tashoshin mota.

Kwamishinan, wanda ya samu wakilcin Ibrahim Nasir Bunkure, Daraktan Kula da Gurbacewar Muhalli na ma’aikatar, ya ce sun shawarci ’yan kasuwar kan yadda za su tsaftace kasuwar, musamman la’akari da yadda jini ke taruwa waje guda, wanda hakan ka iya haifar da cututtuka.

Haka kuma, ma’aikatar ta yi kira gare su da su gaggauta share magudanan ruwan kasuwar domin kauce wa ambaliya.

Da yake nasa jawabin, Sarkin Kasuwar, Muhammad Iliyasu Mahadi, ya ce za su yi amfani da shawarwarin da ma’aikatar ta ba su cikin gaggawa.

Wakiliyar mu, Halima Wada Sinkin, ta ruwaito cewa Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi da Albarkatun Ruwa ta Jihar Kano ta gargadi ’yan kasuwar da su guji yanka dabbobin da ake shigo da su kasuwar, tare da tabbatar da lafiyarsu kafin a yanka su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!