Connect with us

Labarai

Amurka ta kama mutane 10 ‘yan Najeriya da aikata laifuka

Published

on

Hukumar Shige da Fice ta Amurka, ICE, ta fitar da sabbin sunayen ƴan Najeriya 10 da take shirin kora daga ƙasar bisa zargin aikata laifuka.

An wallafa sunayen mutanen ne a shafin ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka, DHS, mai taken “Worst of the Worst”, wato “mafi muni cikin masu laifi”.

Laifukan da aka lissafa sun haɗa da zamba da satar bayanai, laifukan da suka shafi cin zarafinn yara, laifukan miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar makamai.

Bayanan da aka wallafa a shafin na DHS, an bayyana su a matsayin baƙin haure da ICE ta kama bisa laifukan da ake zarginsu.

Ma’aikatar ta ce ƙarƙashin jagorancin DHS, jami’an ma’aikatar da ICE suna aiwatar da alƙawarin Shugaba Donald Trump na korar ɗimbin baƙin haure daga Amurka, inda suka fara da waɗanda ta bayyana a matsayin masu aikata manyan laifuka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!