Labarai
DSS ta kama shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Bello Bodejo bayan EFCC ta sake shi

Lauyoyin shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta ƙasa, Bello Bodejo, sun zargi hukumar DSS da sake kama shi jim kaɗan bayan da hukumar EFCC ta sake shi.
Lauyan Bodejo, Muhammad Sharif, ya ce DSS ba ta sanar da su dalilin sake kama shi ba, yana mai cewa za su kalubalanci matakin a kotu.
An sake sakin Bodejo ne a yau Juma’a, bayan ya shafe kusan watanni huɗu a tsare bisa zargin halasta kuɗin haram.
A watan Yuli ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belinsa, bayan EFCC ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume shida, waɗanda ya musanta.
Kotun ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranakun 5 da 6 da kuma 7 ga watan Oktoban shekarar nan.
You must be logged in to post a comment Login