Labarai
Gwamnatin Kano ta yi haɗin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya da EU kan sarrafa sharar makamashi

Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Hukumar Raya Masana’antu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNIDO) da Tarayyar Turai (EU) domin inganta sarrafa sharar kayayyakin makamashi mai sabuntawa da kuma bunƙasa tattalin arziƙin Circular Economy.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan yayin buɗe wani taron horaswa na kwana biyu a Kano kan tsarin tattara bayanai da sa ido kan yadda ake sarrafa sharar kayayyakin samar da wutar lantarki ta hasken rana da sauran makamashi masu sabuntawa.
Ya ce yayin da ake ƙara amfani da makamashi mai tsafta, yana da muhimmanci a tabbatar da an tsara yadda za a sarrafa tsofaffin kayayyakin da suka haɗa da batir, farantan hasken rana da na’urorin canza wuta, domin kare muhalli.
Dakta Hashim ya ce gwamnatin Kano na ci gaba da aiwatar da manufofin kare muhalli, inganta tsarin sarrafa shara da kuma dasa bishiyoyi miliyan 10 a bana.
Ya kuma ce ana shirin farfaɗo da masana’antar samar da takin gargajiya ta Dorayi, tare da kafa cibiyar tattalin arziƙin Circular Economy a Gabasawa, wadda ake sa ran za ta kasance cikin manyan cibiyoyin irin wannan a Najeriya.
A cewarsa, Kano a shirye take ta ci gaba da aiki tare da UNIDO da EU da sauran abokan hulɗa wajen inganta tsarin sake amfani da kayayyaki, tattara bayanan muhalli da kuma sarrafa sharar kayayyakin makamashi mai sabuntawa.
You must be logged in to post a comment Login