Connect with us

Labarai

Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kwaso mutanen da ke Afirka ta Kudu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce za ta ci gaba da kwaso ’yan ƙasar daga Afirka ta Kudu, inda ake samun fargabar hare-haren ƙyamar baƙi dab da zanga-zangar da ake shirin yi a gobe Talata 30 ga Yuni.

 

Rahotonni sun bayyana An ce wani jirgin Air Peace ya tashi daga kasar nan a safiyar yau Litinin, tare da shirin kwaso wasu daga cikin ’yan ƙasar nan zuwa Legas.

 

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya Kimiebi Ebienfa, ne ya bayyana hakan inda ya ce wannan mataki na daga cikin shirin gwamnati na ba da dama ga ’yan ƙasar nan da ke son dawowa gida cikin aminci.

 

Bayanai sun tabbatar da cewa fiye da ’yan Najeriya 700 na maƙale har yanzu a Afirka ta Kudu, kwanaki kaɗan kafin wa’adin da wasu ƙungiyoyin masu ƙyamar baƙi suka bayar ya cika.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!