Connect with us

Labarai

Gwamnan Beneu ya buƙaci jami’an tsaro su yi bincike kan kisan jagoran makiyayan jihar

Published

on

Gwamnan Jihar Beneu, Hyacinth Alia ya buƙaci jami’an tsaron jihar su gaggauta gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa jagoraan makiyayan jihar Alhaji Arɗo Risku da wasu suka kashe a jihar ranar juma’a.

 

Cikin wata sanarwa da sakataren ya da labaran gwamnan, Tersoo Kula ya fitar ya ce gwamnan ya bayar da umarni kamo wadanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

 

Gwamnan ya buƙaci hukomomin jihar su yi aiki tare da jagororin al’ummar jihar domin tabbatar da zaman lafiya.

 

Haka ma gwamnan ya buƙaci mambobin ƙungiyar MACBAN da na sauran al’umma su kwantar da hankali domin bin doka da oda.

 

Daga ƙarshe gwamnan ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da duka mambobin ƙungiyar makiyaya ta MACBAN.

 

Rundunar yansandan jihar ta ce ta kama wasu mutum 10 bisa zargin hannu a kisan Arɗo Risku.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!