Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar yaki da shaye-shayen kayan maye
Gwamnatin jihar Kano na shirin kafa wata hukumar yaki da shaye-shayen kayan maye a jihar baki daya.
Kwamashinan sharia na jihar Kano, Barista Ibrahim Mukhtar ne ya bayyana hakan a yau Talata jim kadan bayan kammala shirin ‘Barka Da Hantsi’ na nan Freedom Radio.
Barista Ibrahim Muktar wanda shi ne babban mai shigar da kara na gwamnatin jihar Kano ya ce, idan an kafa hukumar za ta rika gudanar da binciken kayan maye da a yanzu ke neman zama ruwan dare cikin al’umma.
Kwamashinan ya kara da cewa hukumar kuma za ta hada hannu da sauran hukumomin da musamman ke gudanar da ayyukan da suka shafi tsaftace mu’amalar jama’a don tabbatar da magance matsalolin shaye-shaye a jihar Kano.
Ya ce za a kafa hukumar ne da nufin kange jama’a daga shiga harkar shaye-shayen, inda kuma ya yi kira ga iyaye da su rika kulawa da tarbiyyar ‘ya’yan su tare da basu ilimi don rage irin fadawa amfani da miyagun kwayoyi da sauran kayen dake sa maye.