Labarai
Gwamnatin Kano za ta kashe fiye da miliyan 150 don sake gina masallacin da wani matashi ya kona

Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe fiye da naira miliyan dari da hamsin da daya domin sake gina Masallacin da wani matashi ya kona tare da masallata a garin Gadan dake karamar hukumar Gezawa a ranar 16 ga watan Mayun bara.
Hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar.
Sanarwar ta ce, ginin zai hadar da na makarantar Islamiyya da Ofisoshi da kuma gyaran bandakuna tare da samar da wutar Sola da kuma famfon tuka-tuka.
Gyaran masallacin na daga cikin alkawarin da gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi wa alummar garin na Gadan lokacin da ya kai ziyara na cewar zai gudanar da gyaransa.
Haka kuma, ta cikin sanarwar gwamnan ya bukaci al’ummar yankin na Gadan da su bayar da hadin kan da ya kamata wajen tabbatar da aikin tare da kula da shi idan an kammala.
You must be logged in to post a comment Login