Labarai
Gwamnatin Kano za ta yi taron jin ra’ayin jama’a da masu ruwa da tsaki

Gwamnatin jihar Kano za ta yi taron jin ra’ayoyin jama’a da masu ruwa da tsaki kan sauye-sauyen da ake shirin yi a kundin tsarin mulkin ƙasa, domin fitar da matsayar jihar kafin zaman sauraron ra’ayoyi na majalisar dattawa.
Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce, an gayyaci wakilan majalisar jiha da ta tarayya da kungiyoyin fararen Hula da kafafen yaɗa labarai da ‘yan kasuwa da shugabannin addini da na gargajiya.
Haka kuma, sanarwar ta kara da cewa, an gayyaci ƙungiyoyin kwadago da ƙwararru irinsu Kungiyar Lauyoyi NBA da Kungiyar yan Jarida NUJ da kungiyar Direbobi NURTW da Kungiyar Malamai NUT da Kungiyar Likitoci NMA.
Haka kuma sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran halartar duk masu riƙe da mukaman siyasa na Kano da tsofaffi.
Taron zai gudana a ranar Alhamis 24 ga Yuli ga watan nan da muke ciki da misalin karfe 1:00 na rana a dakin taro na Coronation Hall da ke Fadar Gwamnatin Kano.
You must be logged in to post a comment Login