ilimi
Gwamnatin Kano zata biyawa daliban Jami’ar Bayero su 7000 kudin makaranta
Gwamnatin jihar kano ta ce zata biyawa ɗaliban da suke karatu a jami’ar Bayero adadin su Dubu Bakwai kuɗin makaranta sakamakon matsi da wahala da ɗaliban suke ciki na ƙarin kuɗi da jami’ar tayi.
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan ta bakin kwashinan yaɗa labarai Baba Halilu Ɗantiye a daren jiyan bayan kammala zaman zartarwa da gwamnatin ta gudanar a jiya kan batutuwan da suka shafi gwamnati.
Baba Halilu Ɗantiye ya kuma ce ‘la’akari da yadda ɗalibai suke ta kokawa kan ƙarin kuɗin yasa gwamnati ta ɗau nayin biyan kuɗin’.
Ɗan Tiye ya kuma ce ‘gwamnatin ta ƙara ware kuɗi Miliyan dari da Tamanin da za’ayi gyaran titunan da suka lalace sakamakon ruwan sama’.
Freedom Radio ta rawaito cewa gwamnatin ta ƙara ware adadin kuɗi sama da miliyan 30 domin zagaye filin idi sai kuma kudi Miliyan Ɗari Takwas da hamsin da Hudu da za’ayi auren zawarawa da su.
Rahoton: Umar Abdullahi Sheka
You must be logged in to post a comment Login