Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano zata fara amfani da dokar aikin gwamnati ta hanyar fasahar sadarwa

Published

on

 

Gwamnatin jihar Kano na shirin samar da dokar da zata bada cikakkiyar damar aiwatar da tsarin gudanar da aikin gwamnati ta amfani da fasahar sadarwa a duk fadin jihar, domin saukaka ayyukan gwamnati da bunkasa fannin tattalin arzikin ta amfani da fasahar sadarwa.

 

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a wajen rufe taron Majalisar Sadarwa, kirkira da fasahar sadarwa Karo na 11, wanda ya gudana a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati Kano.

 

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya aikewa manema labarai ya ce, tsare-tsaren an samar da su ne da nufin tabbatar da daidaito, inganci, da kuma tabbatar da gaskiya wajen tafiyar da harkokin kudaden gwamnati ta hanyar amfani da manhajoji don tabbatar da taka tsantsan wajen amfani da kudaden.

 

 

Ya kara da cewa tun bayan hawansa mulki, gwamnan kano ya samu damar sake bude Cibiyar fasahar sadarwa da aka rufe, biyan albashi na hanyar zamani, inganta tsarin biyan kudin IGR da nufin toshe zurarewar Kudade da dai sauransu .

 

Abba Kabir Yusuf ya bukaci da a mikawa jihar Kano matattarar fasahar sadarwa ta NCC dake jihar domin yin amfani da shi yadda ya kamata, ya kuma kara jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da gudanar da ayyukan da za su ciyar da jihar Kano gaba musamman ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki .

 

Tun da farko, ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki ta fasahar sadarwa, Dokta Bosun Tijjani, ya ce an shirya taron ne bisa la’akari da ajandar sabunta fata ta Shugaba Tinubu, sanin karfin fasaha da kirkire-kirkire a matsayin masu samar da ci gaban tattalin arziki da kuma bunkasar tattalin arzikin Nigeria.

 

Ya ci gaba da cewa, domin a kara habaka sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar inganta samar da kayayyaki a sassa masu muhimmanci ta hanyar fasaha da kere-kere, an samar da wani tsari wanda ya kunshi ginshikai biyar na ilimi, manufofi, ababen more rayuwa, kirkire-kirkire, kasuwanci da jari.

 

Dokta Bosun Tijjani ya ce kowane ginshiki na da nasaba da manufofin gwamnati da kuma cudanya da sauran jama’a, wanda shi ne tushen dabarun ba da damar ci gaban tattalin arziki da ci gaban fasahar sadarwa a kasar nan.

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!