Labaran Kano
Gwamnatin Kano zata sabunta tallafin ilimi na shekara 5 da kasar Faransa
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin sa zata sabunta yarjejeniyar ilimi tsakaninta da gwamnatin kasar Faransa, karkashi tallafin ilimi na Kano da Faransa, na shekaru 5 wanda zai fara aiki daga shekara ta 2020.
An dai fara wannan yarjejeniya ne a shekara ta 2016.
Gwamnan ya ce Karin na shekaru 5 da aka samu a yanzu, domin baiwa daliban da zasu cigaba da digirinsu na uku, damar cigaba da karatunsu,ko da kuwa basu sami damar kamala karatunsu ba a zangon farko.
Wannan dai na kunshe cikin wata sanarwa da sakataren gwamna Abba Anwar ya fitar a jiya.
Sanarwa ta yaba da tsarin ilimin tsakanin gwamnatin Kano da gwamnatin Faransa, inda ya ce wannan wani shiri na inganta harkar ilimi.
Ya ce a cikin shirin alal misali an tsari shi ne domin inganta malaman jami’oi wanda zasu dawo gida su kuma inganta harkar koyarsu ga dalibai a nan gida.
Gwamna ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga dalibai jihar Kano wanda suka samu tallafin karatu suke kuma kasar ta Faransa, a birnin Paris a jiya, ya kara da cewa gwamnatinsa na kokarin inganta ilimi a dukkanin matakai.
Ganduje ya kara da cewa ya zama wajibi ayi wa harkar ilimi garanbawul , tun daga tushe a don haka ne aka mayar da ilimin ya zama kyauta kuma dole ga dukkanin yan makarantar firamare da sakandare.
Wanda tuni aka fara aiwatar da hakan, a wani yunkurin samar da dalibai masu kwazo a firamare da sakandare, a yanzu kuma ake kokarin inganta makarantar gaba da sakandare.
Da take Magana wata daliba da take koyon aiki a ofishin jakadancin Faransa a Najeriya Mrs Laila Matthew ta bukaci gwamna Ganduje da hallarci ranar Najeriya da za’a gudanar a Faransa inda yan Najeriya da suke neman ilimi a Faransa daga jami’oi daban-daban zasu gana wasu dalibai na faransa domin karawa juna sani.