Labarai
Gwamnatin Kano zata samar da doka kan gurbacewar mahalli
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta mika doka ga majalisar dokokin jihar Kano domin dakile matsalolin da ke janyo gurbacewar muhalli a fadin jihar nan.
Kwamishinan ma’aikatar muhalli na jihar ta Kano Dr. Kabiru Ibrahim Getso
ne ya bayyana haka bayan kare kunshin kasafin kudin ma’aikatar sa gaban kwamitin kula da muhalli na majalisar dokokin jihar Kano a yau.
Ya ce ko da ya ke gwamnati ba ta gamsu da rahoton da wata kungiya ta fitar a baya-bayan nan da ke alakanta Kano a matsayin birni mafi gurbacewar muhalli ba amma hakan ba zai sa ta yi watsi da shirinta na dakile illolin muhalli.
A wani labarin Kuma Attorney janar na jihar Kano kuma kwamishinan sharia, Barrister Ibrahim Mukhtar, ya ce gyaran dokar hukunta manyan laifuka ta jihar Kano za ta fara aiki gadan-gadan domin rage matsalolin da ake fuskantar bangaren shari’a.
Barrister Ibrahim Mukhtar ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai bayan kare kunshin kasafin kudin ma’aikatar ta shari’a.
A nan kuma jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Kano da ke garin Wudil, ta ce za ta kashe sama da biliyan daya da rabi a shekara wajen gudanar da ayyuka da nufin bunkasa harkokin karatu a Jamiar.
Kai tsaye: An dage cigaba da zaman majalisar Kano
Yaran Kano: Majalisar dokokin Kano zata dauki mataki
Kai tsaye: An Kammala tantance sunayen kwamishinoni -Majalisar Kano
Mataimakin shugaban Jamiar mai kula da harkokin karatu, farfesa Aminu
Umar Fagge ne ya bayyana haka bayan kare kunshin kasafin kudin Jamiar a majalisar dokokin jihar Kano a yau.
Wakilin mu na majalisar dokokin Kano Abdullahi Isah ya ruwaito shugaban
kwalejin nazarin shari’a da addinin musulunci na Aminu Kano farfesa
Abubakar Balarabe Jakada na cewa za su kashe sama da biliyan daya a shekara mai zuwa domin gudanar da ayyuka da za su kawo ci gaban kwalejin.