Labarai
Gwamnatin Kano zata sauya fasalin samar da gidaje
Gwamnatin Kano ta ce zata maida hankali wajen samar da gidaje a jihar nan.
Sabon kwamishinan gidaje da sufuri na jihar Kano Barrister Musa Abdullahi Lawan ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kama aiki.
Barrister Musa Abdullahi Lawan ya ce zai yi aiki da kudororin gwamnatin Ganduje wanda zai inganta rayuwar ‘yan jihar Kano.
“Zamu yi duk mai yuwa wajen inganta samar da karancin gidaje da kuma gina rukunin gidajen a nan Kano don wadata ‘yan asalin jihar nan da gidaje a cewar sa”
Muna rokon gwamna Ganduje ya sulhunta Muntari da Sha’aban –Habib Sadam
Ganduje da Sarkin Kano sun gana da masu zuba jari daga kasar China
Ganduje ya hana iyayen yara Magana da yan jarida
Ka zalika sabon kwamishinan ya ce Allah ya wadata jihar nan da filaye kasancewar hakan ya sanya masu zuba jari ke tururuwa don zuba jari a nan Kano.
Ya kuma yi alkawarin sake nazari kan harkokin sufuri a jihar nan wanda zai yi dai-dai da na zamani
Har ila yau, Barrister Musa Abdullahi ya ce za’a samar da kayan sawa na bai daya ga masu harkokin sufuri da kuma fantin mota ta yadda jihar Kano zata yi gugayya da sauran kasashen waje ta fuskar sufuri.