Labarai
Gwamnatin kano zata tallafawa Almajirai da sanaoin dogaro da kai

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta yi hadin gwiwa da babban bankin kasa CBN domin samun rancen kuɗin da za ta sayi na’urar cirar kuɗi ta P.O.S a fadin jihar.
Tsohon sakataren gwamnatin Kano Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi, wanda kuma ya wakilci gwamnatin Kano a wajen taron wayar da kan malaman tsangaya.
Ya ce, za a ranci kuɗin ne wajen tallafawa dukkanin makarantu na tsangaya a jihar Kano, ta hanyar samarwa da ɗaliban sana’o’in dogaro da kai.
A cewar sa, gwamnatin ta kirkiro da tsarin ne domin a rage yawaitar barace barace a kan tituna.
Alhaji Sulaiman ya kuma ce, gwamnatin ta hada kai da babban bankin ƙasa domin a bude wuraren cire kudi ta cikin sauki ba sai mutun yaje banki ba.
You must be logged in to post a comment Login