Kasuwanci
Gwamnatin Kano zata Zamanantar da hanyoyin samar da Madarar Shanu
Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar dacewar nan da ‘yan watanni masu zuwa zata samar da sabon tsari na zamani wajen yawaita samar da madara shanu a jiha.
Shirin zai kasance karkashin shirin bunkasa Noma da kiwo na jihar Kano da bankin musulunci da asusun Lives and Livehood Fund ke daukar nauyi gudanar dashi.
Shugaban gudanar da shirin bunkasa Noma da kiwo na jiha Malam Ibrahim Garba , ya bayyana haka a yau Talata lokacin da ya karbi bakuncin Kungiyar masu Fura da Nono karkashin jagorancin masu sai da Madara ta jiha a ofishin sa.
Labarai masu Alaka.
Shirin Bunkasa Noma da Kiwo na jiha zai fara yiwa dabbobi Allura ta Rigakafi
Gwamantin Kano ta kaddamar da kwamitin bunkasa harkokin noma
Malam Ibrahim Garba , kamar yadda sanarwar kakakin shirin Aminu Kabir Yassar ya ruwaito , ya ce shirin an tsara shi ta hanyar samar da guraren tara Madara 200 tare da ingantasu a Zamanan ce da bada tallafi da dabarun aiwatar wa ga kungiyoyin.
Malam Ibrahim Garba, ya kara dacewa tsarin zai samar da rage lalacewar Madara da asarar da masu ita suke , tare da adana Madarar wanda hakan zai taimaka matuka wajen samar da Madara mai inganci da kudaden shiga ga Makiyaya da dillalai.
Shugaban shirin yace bayan guraren adana Madarar , za a samar da wajen yin Allurar rigakafi ga shanu don tabbatar da lafiyar su wajen samun madara mai lafiya da inganci.Ya kuma yi kira ga ‘yan kungiyar ta Fura da Nono da suyi aiki kafada da kafada da shirin bunkasa Noma da Kiwo don ganin san samu cigaba da bunkasa tsarin a fadin jiha
Da yake nasa Jawabin shugaban Kungiyar Fura da Nono Alhaji Lawan Muhammad , ya ce sun kawo ziyarar ne don ganin an samu hadin kai tare da bayar da gudumowar kowanne dan kungiyar su wajen ganin shirin ya samu kafuwa a jiha.
Inda yace sun zo neman shawarwari tare da sanin manufofi da tsarin da aka tanada na samar da madara mai inganci da sanin rawar da zasu taka wajen inganta samar da madarar da kasuwancin ta.
You must be logged in to post a comment Login