Labarai
Gwamnatin Katsina ta karɓi ƴan matan da aka kuɓutar a Zamfara
Gwamnatin jihar Katsina ta karɓi ƴan mata 26 da aka kuɓutar daga ƴan ta’adda a hannun gwamnatin Zamfara.
Gwamnan jihar Aminu Bello Masari ne ya karɓi ƴan matan a daren Lahadi a fadar gwamnatin jihar.
“babu sauran sassauci ga duk ƴan bindigar da ke hallaka mutane a yankunan jihar” a cewarsa.
Gwamnan ya kuma yi godiya ga gwamnatin Zamfara kan kuɓutar da ƴan matan.
Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na Zamfara Abubakar Justice Dauran ne ya jagoranci tawagar miƙa ƴan matan.
Ya ce, “Gwamnati ta samu nasarar kuɓutar da ƴan matan ne ta hanyar bayanan sirri da tubabbun ƴan ta’adda suka bayar”.
Dauran ya ƙara da cewa, Gwamnan Zamfara ya ɗinka musu kaya saboda mafi yawa an same su tsirara.
Sannan gwamnan Zamfara ya bai wa kowacce kyautar Naira dubu goma-goma.
Labarai masu alaka
Da ɗumi-ɗumi: An ceto ƴan mata daga hannun ƴan bindiga a Zamfara
Zamu hukunta duk basaraken da ya fita daga Zamfara – Matawalle
You must be logged in to post a comment Login