Labarai
Gwamnatin Katsina ta kashe fiye da Biliyan 36 a harkar tsaro

Gwamnatin jihar Katsina da hadin guiwa da kananan hukumomin jihar 34 sun kashe kimanin Naira bilyan 36 da miliyan dari 8 inganta harkokin tsaro a sassan jihar.
Mataimakin Gwamnan jihar, Faruk Lawal Jobe, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a jihar inda ya ce, an kashe kudaden ne tun daga lokacin da gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda ta hau mulki a shekarar 2023 har zuwa yanzu.
Lawal Jobe ya kuma ce an yi amfani da kudaden ne wajen sayen motoci masu sulke guda 10 da motocin samfurin Toyota Hilux guda 65 da kuma babura guda 700.
Mataimakin gwamnan ya kara da cewa gwamnati ta kashe Naira miliyan 985 da dubu 900 wajen samar da magunguna da kuma tallafin kudi da sauran hanyoyin agaji ga wadanda suka samu raunika sakamakon ayyukan ta’addanci a jihar.
You must be logged in to post a comment Login