Labarai
Gwamnatin Katsina ta tabbatar da mutuwar mutane 2 sakamakon zazzabin Lassa

Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon kamuwa da zazzabin cutar Lassa.
Jaridar The Punch ta rawaito cewar guda daga cikin likitocin dake kula da cutuka masu yaduwa a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake jihar ta Katsina dakta Muhammad Abubakar ne ya bayyana hakan.
Ya kuma ce zuwa yanzu mutane uku ne aka samu rahoton sun kamu da cutar inda biyu suka rasu.
You must be logged in to post a comment Login