Labarai
Gwamnatin Katsina zata tura dalibai 40 kasar Masar
Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta ware guraben karatu 40 ga ɗalibai ƴan asalin jihar waɗanda za ta tura ƙasar Masar domin karatu a fannin likitanci.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne a lokacin taron majalisar zartarwar jihar wanda gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya jagoranta.
Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, Farfesa Abdulhamid Ahmed ya ce ‘ƙananan hukumomi 31 za su bayar da sunayen dalibai ɗai-ɗaya, yayin da garuruwan Daura da Funtua za su bayar da sunayen dalibai bibbiyu’.
‘Inda a za’a debi ɗalibai uku cikin ƙwaryar birnin Katsina’.
Sai dai sanarwar tace iya daliban da suka kammala makarantun Gwamnatin ne kadai zasu iya cin gajiyar wannan tsarin tsarin.
Rahoton: Yusuf Sulaiman
You must be logged in to post a comment Login