Labarai
Gwamnatin Najeriya ta amince da bin umarnin kotun koli na dage ranar data sanya na daina amfani da tsohon kudi
Gwamnatin Najeriya ta ce, za ta mutunta umarnin da Kotun Kolin kasar nan ta bayar na kara wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi na naira 200 da 500 da kuma 1,000 a yau 10 ga watan Fabrairu.
Umarnin ya biyo bayan karar da wasu gwamnonin jihohi uku suka shigar kan bukatar dakatar da wa’adin.
A ranar Laraba ne dai kotun ta bayar da umarnin inda ta ce a dakata da amfani da wa’adin har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu lokacin da za ta yanke hukunci a kan shari’ar da gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zmfara suka shigar suna kalubalantar wa’adin.
Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan gwamnatin Najeriya Abubakar Malami, ne ya ce gwamnatin za ta bi umarnin a yayin wata hirarsa da tashar talabijin ta Arise TV jiya Alhamis.
Sai dai ministan ya ce yana fatan idan aka koma sauraren shari’ar Kotun Kolin za ta soke wannan umarni, ta hanyar barin Babban bakin kasa CBN ya aiwatar da tsarinsa na sanya wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudin da bankin ya sauya.
Abubakar Malami ya kuma ce, gwamnati ta yanke shawarar bin umarnin Kotun Kolin ne domin mutunta doka da oda.
Labarin: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login