Connect with us

Labaran Wasanni

Gwamnatin Najeriya ta zabi Gbenga Elegbeleye a matsayin wanda zai jagoranci ‘yan-wasa a winter Olympics

Published

on

Gwamnatin Najeriya ta zabe tsohon Babban Daraktan kwamitin wasanni na kasa Gbenga Elegbeleye, a matsayin wanda zai jagoranci ‘yan-wasa a gasar winter Olympics da za’a gudanar a Pyeong Chang na kasar Koriya ta Kudu, wanda za’ a fara ranar 9 zuwa 28 ga watan Fabrairu mai ka mawa.

shugaban kwamitin Olympics na kasa, Habu Gumel ne ya bayyana hakan a jiya a taron karrama wasu ‘yan-wasan Olympics din kasar nan da ya gudana a birnin tarayya Abuja.

Shugaban hukumar Olympics din Habu Gumel ya ce sauran yan wasan da suke zama a kasar Amurka zasu shigo Najeriya a ranar Larabar nan daga nan su tashi zuwa kasar Koriya ta kudu.

‘yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle mata hudu ne za su wakilci Najeriya a gasar wadanda da suka hadar da Simidele Adeagbo da Seun Adigun da Ngozi Onwueme da kuma Akuoma Omeoga.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!